Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli

- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Honourable Justice Uwani Musa Abba Aji, JCA a matsayin mai shari’a a kotun kolin Najeriya

- Hakan ya biyo bayan tattaunawa da dama da suka yi bayan dan jinkiri da aka samu wajen tabbatar da ita

- Tun da farko dai an dakatar da tabbatar da ita din ne sakamakon zarginta da aka yi da amsar rashawa

Majalisar dattawan Najeriya a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba ta tabbatar da nadin Honourable Justice Uwani Musa Abba Aji, JCA a matsayin mai shari’a a kotun kolin Najeriya bayan tattaunawa da dama.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wanda yayi magana bayan tabbatar da nadin ya taya Abba-Aji murnar wannan sabon mukami da ta samu.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli
Source: Depositphotos

A ranar Talata, 16 ga watan Oktoba ne kungiyar alkalan kasar (NJC) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da kira akan kin zabar Uwani Abba-Aji a matsayin mai shari’a a kotun koli kan zargin aikata rashawa.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa

Kungiyar NJC tace an wanke Abba-Aji wacce aka bincika kan zargin amsar kudi daga wani lauya daga zargin da ake mata a yanzu bata fuskantar kowani tuhuma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel