Jam’iyyun siyasa na neman a basu kudi don su amince da Buhari – Oshiomhole

Jam’iyyun siyasa na neman a basu kudi don su amince da Buhari – Oshiomhole

- Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyun adawa da dama na ta neman a biya su kudi domin su amince da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararsu

- Ya nuna bakin ciki kan yadda jam’iyyun siyasa ke samar da wata kafa na siyan kuri’u a zaben shekara mai

- Ya kuma karyata zargin jam’iyyar adawa na cewa suna kokari yin magudi a zaben 2019

Gabannin zaben 2019, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyun adawa dad a na ta neman a biya su kudi domin su amince da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararsu sannan su yi aiki domin nasararsa.

Oshiomhole wanda ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Turai a sakatariyar APC da ke Abuja ya nuna bakin ciki kan yadda jam’iyyun siyasa ke samar da wata kafa na siyan kuri’u a zaben shekara mai zuwa domin basa duba cancantar yan takara a zaben sai dai amincewa da jam’iyyun siyasa masu jakar kudi.

Jam’iyyu siyasa a neman a basu kudi don su amince da Buhari – Oshiomhole

Jam’iyyu siyasa a neman a basu kudi don su amince da Buhari – Oshiomhole
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa: “INEC tayi kokarin kin yiwa jam’iyyun siyasa rijista, amma sai bangaren shari’a tace bah aka ba ana iya yiwa duk wanda ke son rijista amma abun shine muna da dogon takardar kada kuriu’a wanda shine kalubale a ranar zabe ta yadda mutane za su gane wanda za su zaba.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa

“Zan iya fadin tayi nawa na samu daga wadannan jam’iyyun siyasar cewa idan zan iya biyan adadin kudi kaza zasu sanar da goyon bayansu ga dan takarar ka. Don haka mutane sun kafa jam’iyyun siyasa a matsayin wajen kasuwanci.

Ya kuma karyata zargin jam’iyyar adawa na cewa suna kokarin yin magudi a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel