Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya 'yan majalisar da suka yiwa shugaba Buhari iyu yayin gabatar da kasafin kudin 2019 basu samu tarbiya daga iyayensu ba

- Yahaya Bello ya ce 'yan majalisun da suka rika ihun ba su kishin kasa kuma makiya demokuradiyya ne da Najeriya

- Gwaman ya kuma jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kan namijin kokarin da ya ke yi domin kawo cigaba a Najeriya

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce 'yan majalisun da suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu yayin da ya tafi gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 a jiya Laraba mutane ne da iyayen su ba su basu tarbiyya ba tun suna yara.

A hirar da gwamnan ya yi da manema labarai a gidan gwamnati bayan bikin Anchor Borrowers Programme da akayi a daren Laraba, ya ce 'yan majalisar sun dau alwashin lalata Najeriya ne saboda tsabar son zuciya.

Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

Idan ba a manta ba dai a jiya Laraba ne wasu 'yan majalisun tarayya na jam'iyyun adawa suka rika yiwa shugaban kasar ihu a duk lokacin da ya lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu a yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin na 2019.

A kalaman da ya fada domin kare Buhari, gwamnan ya ce, "Akwai mutane guda biyu. Babban mu mai halin dattaku da kishin kasa, shugaba Muhammadu Buhari sai kuma wasu mutane masu son kai da ke da niyyar lalata Najeriya da demokuradiyya kuma sun nuna kansu a yau.

"Kamar yadda na fadi a baya, idan ka samu yaron da iyayensa ba su bashi tarbiya ba, zai zama fitina ga al'umma. Irin abinda muka gani kenan a majalisar tarayya a yau.

"Ya kamata ace 'yan majalisun mutane ne masu dattaku da nagarta. Amma mun ga irin mutanen da ke majalisar dattawa a yau.

"Sai dai ya godewa Allah kuma na gode wa shugaba Muhammadu Buhari bisa yada ya gabatar da kasafin kudin na shekarar 2019 wadda mu kayi imanin cewa zai daukaka Najeriya zuwa mataki na gaba da izinin Allah."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel