Gaskiyar Magana: Soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa - Osinbajo

Gaskiyar Magana: Soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa - Osinbajo

- Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa

- Osinbajo ya kambama mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayinda ya cika shekaru 76 da haihuwa

- Shugaban kasa Buhari tare da abokin takararsa Osinbajo, na neman tazarcen kujerunsu ne a babban zaben 2019 da ke gabatowa

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya kambama mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayinda ya cika shekaru 76 da haihuwa a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba, 2018.

Osinbajo wanda ya ke a garin Vienna, kasar Austia, inda ya je halartar taron shuwagabannin Afrika da nahiyar Turai, inda ya hadu da sauran shuwagabannin gwamnatocin kasashe da dama, ya bayyana Buhari a matsayin adalin mutum wanda soyayyarsa ga 'yan Nigeria bata misaltuwa.

Shugaban kasa Buhari tare da abokin takararsa Osinbajo, na neman tazarcen kujerunsu ne a babban zaben 2019 da ke gabatowa, wanda zai gudana a cikin watan Fabrerun 2019.

KARANTA WANNAN: 2019: Amfani da jami'an soji wajen murdiyar zabe zai haddasa tashin hankali - Ezekwesili

Gaskiyar Magana: Soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa - Osinbajo

Gaskiyar Magana: Soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa - Osinbajo
Source: Facebook

Da yake mika sakon taya shugaban kasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Osnbajo ya wallafa wani muhimmin sako a shafinsa na Twitter, inda yake cewa: "Zuwa ga wannan mutumin, wanda kowa zai buga misali da shi a fagen yiwa 'yan Nigeria aiki tukuru.

"Zuwa ga wannan mutumin, wanda yake cikakken adali, mai cike da karsashi, wanda kuma soyayyarsa ga 'yan Nigeria bata misaltuwa, kuma ta gaskiya ce. Barka da cika shekaru 76 a duniya," a cewar Osinbajo.

An haifi shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura, a ranar 17 ga watan Disambar 1942, bayan kammala karatunsa a garin Daura da Katsina, ya shiga aikin soji a 1961. Tun daga shekarar 2003 shugaban kasa Buhari ke tsayawa takarar shugabancin kasar amma bai samu nasara ba, har sai a zaben 2015, idan ya kayar da Goodluck Jonathan, shugaban kasar mai ci a wancan lokaci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel