Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa

Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa

- Daya daga cikin yan majalisar da suka yi wa Buhari ihu a majalisar dokokin kasar a ranar Laraba ya bayyana dalilinsu na yin haka

- Kinsley Chinda, ya bayyana cewa sun gwale shugaban kasar ne saboda mafi akasarin abubuwan da yayi ta fadi game da yanayin da kasar ke ciki ba gaskiya bane

- Yace kalaman shugaban kasar cike suke da tufka da warwara, musamman idan aka zo batun yin aiki da kasafin kudi

Labarin da ke zuwa mana ya nuna cewa daya daga cikin yan majalisar da suka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ihu a majalisar dokokin kasar a ranar Laraba ya bayyana dalilinsu na yin haka.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Kinsley Chinda, dan Majaliasa daga jihar Rivers, ya bayyana cewa sun gwale shugaban kasar ne saboda mafi akasarin abubuwan da yayi ta fadi game da yanayin da kasar ke ciki ba gaskiya bane.

A cewarsa kalaman shugaban kasar cike suke da tufka da warwara, musamman idan aka zo batun yin aiki da kasafin kudi.

Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa

Kasafin kudin 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu - Yan Majalisa
Source: Depositphotos

Yace: “Shugaba Buhari ba ya yi mana adalci musamman wajen aiwatar da kasafin kudi. A duk lokacin da ya yi katobara ko ya kasa gudanar da wasu abubuwa, sai ya dora laifin a kan mu ‘yan majalisa.

“Ka ga dai ya kasa gudanar da manyan ayyuka, wanda ya sa ba a yi wasu abubuwan da suka wajaba daga cikin kasafin 2018 masu yawa da muhimmanci ba.

KU KARANTA KUMA: Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC

“To mutumin da ya kasa gudanar da muhimman abubuwa, kuma shi da kan sa ya furta haka, ya kuma zai zo ya dunga ba mu labarin wai ya inganta tattalin arzikin kasa mu kuma mu yarda?

“Shi da kan sa ya ce akwai ayyukan da aka yi kirdadon gudanarwa na naira tiriliyan 6.4, amma hakan bai yiwu ba, sai aka mirgina ayyukan a cikin kasafin 2019, maimakon a yi su cikin na 2018. To ka ga kenan kashi 16 bisa 100 kadai aka gudanar kenan.’’

Dan majalisar ya kara da cewa a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido a hukumomi daban-daban, sun kuma gano cewa da yawan hukumomin ba a sakar musu mafi akasarin kudaden da ya kamata a sakar musu kamar yadda shi Buhari ya rubuta zai yi a cikin kasafin 2018 ba.

Ya kuma yi tsokaci a kan yadda gwamnatin tarayya ke yin biris da dokokin kasa wajen aiwatar da wani abu, da kuma kin bin umarnin kotu.

A karshe ya ce ba ‘yan PDP kadai ba ne suka yi sowa da eho, har da ‘yan APC.

Idan ba za ku manta ba a ranar Laraba, 19 ga watan Disamba ne wasu yan majalisar suka yi wa shugaba Buhari ihu a yayinda yake gabatar da kasafin kudin 2019 a majalisar dokokin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel