Har yanzu a wajen mu su Balogun-Fulani ba ‘Ya 'yan Jam’iyya ba ne – APC

Har yanzu a wajen mu su Balogun-Fulani ba ‘Ya 'yan Jam’iyya ba ne – APC

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta maida martani bayan kotu ta maida Ishola Balogun-Fulani da mutanen Majalisar sa a matsayin shugabannin Jam’iyyar mai mulki a Jihar Kwara.

Har yanzu a wajen mu su Balogun-Fulani ba ‘Ya 'yan Jam’iyya ba ne – APC

APC ta fatattaki Balogun-Fulani daga Jam’iyya duk da umarnin Kotu
Source: Facebook

Sakataren yada labarai na APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, yayi jawabi jiya Laraba 19 ga Wata inda ya bayyana cewa har yanzu matsayar uwar Jam’iyya ba ta canza ba game da korar Ishola Balogun-Fulani da aka yi daga APC.

Kakakin na APC yace an yi amfani ne da tsarin kato-bayan-kato wajen tsaida ‘Yan takara a zabe mai zuwa. A dalilin haka, yace babu abin da zai sa shugabannin APC na Jihar Kwara su shiga cikin harkar zaben tsaida ‘Yan takara.

KU KARANTA: Rigima: Uwar Jam’iyyar APC ta rusa Shugabannin ta a wasu Jihohi

Issa-Onilu ya kara tabbatar da cewa har yanzu a wajen su, Jam’iyya ta kori Balogun-Fulani da mukarraban sa. Onilu yace sunayen wadanda Jam’iyya ta aikawa INEC za ayi amfani da su a zaben 2019 duk da sabon hukuncin kotu.

A jiya ne wani kotu da ke Ilorin yayi watsi da korar da APC tayi wa Ishola Balogun-Fulani da mutanen sa. Kotu tace fatattakar Balogun Fulani da aka yi daga Jam’iyya ba ta zauna ba kuma har yanzu shi ne shugaban APC na ainihi.

Babban Jami’in na APC yace NWC tana da hurumin sallamar duk wanda ta ga dama, don haka tace a daina murde hukuncin da kotu tayi. Onilu yace an fatattaki tsohon shugaban APC na Jihar Kwara ne bayan an same sa da laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel