Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC

Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC

- Manyan APC sun nuna rashin jin dadi akan abunda wasu yan majalisa suka yi wa Buhari

- Yan majalisan dai sun yiwa shugaban kasar ihu ne a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin 2019

- Jiga-jigan jam’iyyar sun sha alwashin daukar fansa akan lamarin

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Cogress (APC) mai sun bayyana rashin jin dadinsu game da ihun da wasu yan majalisa suka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin da ya gabatar da kasafin kudin 2019.

A ranar Laraba, 19 ga watan Disamba ne shugaban kasar ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar dokokin kasar.

Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC

Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC
Source: Facebook

Sun yi wa shugaban kasar ihu ne domin nuna adawa da wasu bayanai na shugaban, yayin da wasu suka rinka sowa domin nuna masa goyon baya.

Honourble Farouk Adamu Aliyu, jigo ne a jam'iyyar ta APC mai mulkin Najeriya, kuma tsohon shugaban marasa rinjaye ne a majalisar wakilan Najeriya, ya ce ya yi mamakin 'tsaurin idon' da ya ce an yi wa wa shugaban kasar.

Tsohon dan majalisar ya ce 'ya'yan jam'iyyar APC za su dauki mataki a siyasance ta hanyar wayar wa al'umma kai domin kada su sake zaben wadanda suka yi wa shugaban ihu.

KU KARANTA KUMA: Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci - Buhari ga yan majalisa

A cewarsa bai kamata a ce 'yan majalisar sun dauki irin wannan mataki kan shugaban kasar ba.

Ya kuma yi zargin cewa shugabannin majalisar wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa su ne ke kokarin tozarta shugaban na Najeriya.

Hon Faruk ya kuma ce 'yayan jam'iyyar APC da suka rinka sowa domin nuna goyon baya ga shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari sun yi ne domin murkushe aniyar 'yayan jam'iyyar adawa ta kunyata shugaban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel