PDP ta tarbi masu sauya sheka daga APC da ADP a Niger

PDP ta tarbi masu sauya sheka daga APC da ADP a Niger

- Jam’iyyar PDP ta tarbi masu sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar ADP a kudancin jihar Niger

- Sama da mutane 1,000 daga APC da kuma 500 daga ADP ne suka koma PDP a jihar ta Niger

- An yi bikin tarban nasu ne tare da fara kamfen din takarar gwamna a jam’iyyar, Umar Nasko a garin Bida

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta tarbi wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da kuma jam’iyyar Advance Democratic Party (ADP) a kudancin jihar Niger.

Jam’iyyar ta tarbi masu sauya shekar ne a Bida hedkwatar yankin inda dan takarar gwamna na jam’iyyar ya fara kamfen dinsa daga yankin da ya zabi mataimakinsa Barrister Mohammed Kudu Ndayeko.

PDP ta tarbi masu sauya sheka daga APC da ADP a Niger

PDP ta tarbi masu sauya sheka daga APC da ADP a Niger
Source: Depositphotos

Masu sauya sheka daga jam’iyya mai mulki karkashin jagorancin Kudu Kasim sun kasance su sama da 1,000 yayinda na ADP suka kasance 500 karkashin jagorancin Yahaya Designer da kuma Adebaye Nupe tare da matasa 300.

Al’umman kananan hukumomi takwas da ke yankin sun fito kwansu da kwarkwatansu domin kaddamar da goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar Umar Mohammed Nasko.

KU KARANTA KUMA: Za mu dauki fansar ihun da aka yi wa Buhari – Manyan jiga-jigan APC

Tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Muazu Babangida Aliyu wanda ya kasance uban jam’iyyar a jihar da shugaban PDP na jihar Tanko Bei da wasu tsoffin jiga-jigan jam’iyyar hudu sun halarci taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel