Ba mu taba tunanin zuba hannun jari a kamfanin Nigeria Air ba – Qatar Airways

Ba mu taba tunanin zuba hannun jari a kamfanin Nigeria Air ba – Qatar Airways

- Kamfanin Qatar Airways ta bayyana cewa ba ta taba sha’awar sa kudi a Nigerian Air ba

- Shugaban kamfanin ya karyata abin da Ministan sufurin jiragen sama ya fada kwanaki

Ba mu taba tunanin zuba hannun jari a kamfanin Nigeria Air ba – Qatar Airways

Shugaban Qatar Airways ya musanya abin da Najeriya ta fada
Source: Facebook

Mun samu labari cewa Kamfanin jirgin saman nan da ake ji da shi a Duniya watau Qatar Airways ya musanya abin da Ministan sufurin jirgin saman Najeriya, Hadi Sirika, ya fada kwanaki na cewa za su sa hannu a Nigerian Air.

Shugaban kamfanin na Qatar Airways, Akbar Al Baker, ya bayyanawa taron manema labarai cewa ba su taba tunanin zuba hannun jarin su a cikin sabon kamfanin Nigerian Air da Gwamnatin Najeriya ke kokarin tadowa ba.

Al Baker yayi wannan jawabi ne a lokacin da ake wani taron Larabawa a cikin babban Birnin Doha da ke Kasar Qatar. Al Baker yace kamfanin na su bai taba wani yunkurin narka kudi a Najeriya ba, yace sam babu wannan batu.

KU KARANTA: Manyan abubuwan da kasafin kudin Najeriya na 2019 ya kunsa

Akbar Al Baker mai shekaru 56 a Duniya wanda shi ne ke kula da kamfanin jiragen sama na Kasar Qatar yace sun ba Jami’an Gwamnatin Najeriya shawara ne kurum game da yadda za a kafa kamfanin jirgin sama a Kasar ba komai ba.

Shugaban kamfann jirgin na kasar Qatar yace iyakar abin da su ka tattauna da Najeriya, shi ne irin jiragen da Kasar za ta saya domin ta ci riba a harkar kasuwanci. Ya kuma ce ko kadan ba su taba tunani sa kudin su a kasuwancin ba.

Kwanakin baya Ministan sufuri, Hadi Sirika, yayi kokarin kafa kamfanin jirgin sama na Gwamnati. A karshe dai dole aka dakatar da shirin bayan yayi ikirarin cewa Qatar Airways da wasu kamfanoni sun nuna sha’awar su shigo ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel