Har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsala – Inji Bukola Saraki

Har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsala – Inji Bukola Saraki

- Shugaban Majalisar Dattawa ya nemi a kawo wani kudiri na tattalin arziki a Najeriya

- Bukola Saraki yayi wannan kira ne bayan Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2019

- Saraki yace karyewar farashin man fetur a Duniya ya girgiza tattalin azikin Najeriya

Har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsala – Inji Bukola Saraki

Saraki yayi magana bayan an mikawa Majalisa kasafin kudi
Source: Depositphotos

Mun ji labari cewa shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Bukola Saraki, yayi wani jawabi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin kasafin kudin 2019 a gaban ‘Yan Majalisar Tarayya jiya a Garin Abuja.

Bukola Saraki ya nuna cewa har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana rawa inda ya alakanta wannan matsala da karyewar farashin gangar man fetur a fadin Duniya. Saraki yace rugujewar tattalin arzikin da aka samu ya taba kasar.

Saraki ya koka da yadda tattalin arzikin Najeriya ya samu kan sa a cikin shekaru 3 da su ka wuce. Shugaban Majalisar yace farashin mai da kuma matsalar rashin tsaro ya kara sa harkar kasuwanci da komai su ka cabe a Najeriya.

KU KARANTA: Kasafin kudin 2019: Gwamnatin Najeriya za ta sake cin bashin Tiriliyan 1.8

Shugaban Majalisar Dattawan yace mutane da-dama sun rasa aikin su a Najeriya a sakamakon rugujewar tattalin arziki da aka samu a Najeriya kwanaki. Sai dai a cewar sa har yanzu kasar ba ta farfado sosai daga wannan matsala ba.

Sanata Saraki yace har yanzu babu wata nasarar kirki da aka samu wajen fadada tattalin arzikin Najeriya inda yace har gobe Najeriya da man fetur ta ke dogaro. Saraki yace Gwamnati ba ta samu kudin da ta sa rai a kasafin 2016 ba.

Sanatan ya kuma koka da halin da Gwamnatin Najeriya ta ke kara jefa kan ta a dalilin cin makukun bashi tare da kuma rage kashe kudi wajen gina abubuwan more kasa. Don haka ne ya nemi a kawo wani kudiri da zai yi tattalin kasar togaciya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel