2019 kowa zai dara: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai, ta ware N305bn

2019 kowa zai dara: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai, ta ware N305bn

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya ce gwamnatin tarayya ta ware N305bn don dawo da tallafin man fetur a Nigeria, wanda aka sanya kudin a cikin kasafin 2019. Buhari dai ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar gaban majalisun dokokin tarayyar kasar, yayin da yake gabatar da kasafin 2019.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta ware akalla N305bn, wanda yayi dai dai da $1bn don baiwa kamfanin NNPC damar sake dawowa da tallafin man fetur a shekarar 2019.

A lokacin da shugaban kasar ke gabatar da kasafin shekarar 2019 gaban majalisun dokokin tarayyar kasar, Buhari ya kuma yiwa 'yan majalisun bayani dalla dalla kan yadda lamarin zai kasance.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba

2019 kowa zai dara: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai, ta ware N305bn

2019 kowa zai dara: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai, ta ware N305bn
Source: Facebook

"A wannan lokaci da muke ciki na durkushewar tattalin arziki, hakika sayen man fetur na zama da wahala, don haka ya zama wajibi mu ragewa 'yan Nigeria wahalhalun da suke fama da su," a cewarsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, shine ya ruwaito cewa gwamnatin Buhari a shekarar 2016, ta janye tallafin man fetur, wanda ya tillasta dilolin man janye hannunsu daga shigowa da man.

Janye hannun 'yan kasuwar man, ya sa kamfanin NNPC ya zamo shi daya tio da ke shigo da mai a kasar, wanda ya haddasa hauhawar farashin litar zuwa N145, har wasu wurare ma N185. Sai dai a yayin gabatar da kasafin kudin, Buhari ya ce gwamnati zata sanya idanu sosai kan kamfanin NNPC na ganin cewa ba ayi almubazzaranci da kudaden tallafin man ba kamar yadda akayi a gwamnatin baya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel