Kungiyar masu saida taki sun ba Buhari gudumuwar Naira Miliyan 570 domin nuna goyon baya a 2019

Kungiyar masu saida taki sun ba Buhari gudumuwar Naira Miliyan 570 domin nuna goyon baya a 2019

- Masu harkar takin zamani sun ba Buhari Miliyan 570 saboda yayi kamfe a 2019

- Kungiyar ta masu saida takin zamani sun ce sun ga canji a Gwamnatin Buhari

- ‘Yan Kungiyar sun yabawa kokarin da Gwamnatin Shugaba Buhari tayi masu

Kungiyar masu saida taki sun ba Buhari gudumuwar Naira Miliyan 570 domin nuna goyon baya a 2019

Fertiliser Producers and Suppliers Association of Nigeria (FEPSAN) tana tare da Buhari
Source: Twitter

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Kungiyar masu hada takin zamani da kuma saidawa a Najeriya, FEPSAN, ta ba Shugaba Muhammadu Buhari babbar gudumuwa yayin da aka dumfari babba zabe na 2019 a Najeriya.

A jiya ne wata Kungiya ta Manoman shinkafa ta shiryawa Buhari liyafa ta musamman a fadar Shugaban kasar na Aso Villa inda masu harkar taki su ka bada gudumuwar Naira Miliyan 570 domin yakin tazarcen Shugaban kasar.

KU KARANTA: Akwai gyara a Nahawun Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo inji wani Farfesa

Kungiyar ta masu hada-hadar taki ta sanar da Shugaba Buhari cewa tana tare da shi a zabe mai zuwa a dalilin irin kokarin da Gwamnatin sa tayi wa harkar gona. Masu harkar takin zamanin su kace sun ga canji daga 2015 zuwa yau.

Shugaban Kungiyar ta FEPSAN watau Thomas Etuh da yake jawabi, ya nuna cewa Gwamnatin Buhari ta babbako da kamfanonin takin zamani da ake su a kasar nan daga 4 zuwa 30 wanda kowane yake aiki yadda ya kamata a yanzu.

Wadanda su ka halarci wannan liyafa da aka shirya sun hada da babban Jigon Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Kwanan nan ne tsohon Gwamna na Legas yayi kira ga mutanen sa da su ba Buhari kuri’a miliyan 6 a zaben badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel