Kisan babban Soja: Rundunar ‘Yan Sanda ta shiga Jihar Nasarawa

Kisan babban Soja: Rundunar ‘Yan Sanda ta shiga Jihar Nasarawa

Labarin da mu ke samu yanzu haka shi ne Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun yi azama sun shirya gano wadanda su ka kashe tsohon babban Hafsun Sojin Najeriya watau Air Chief Marshall Alex Badeh kwanan nan.

Kisan babban Soja: Rundunar ‘Yan Sanda ta shiga Jihar Nasarawa

Sufetan ‘Yan Sanda ya sa a gano Makasan ACM Alex Badeh
Source: Depositphotos

Jami’an tsaron sun bi umarnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na gano Makasan babban Sojan na Najeriya. Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya aika Tawaga guda zuwa Jihar Nasarawa jiya.

Shugaban ‘Yan Sandan Kasar ya tura zuga ta musamman domin bankado wadanda su kayi wa tsohon Sojan saman na Najeriya Alex Badeh, kisan gilla a kan hanyar Keffi a lokacin da yake dawowa daga gonar sa tare da Direban sa.

Jami’in da ke magana da yawun bakin ‘Yan Sandan Najeriya a Yankin Jihar Nasarawa, Kennedy Idirisu, ya bayyanawa manema labarai cewa IGP ya aiko wata runduna ta musamman mai binciken kwa-kwaf a dalilin kisan Alex Badeh.

KU KARANTA: Kwamishinan 'Yan sanda ya gargadi 'yan kasuwa game da bada bashi

Kennedy Idirisu yayi wannan jawabi ne a Garin Lafiya a Jihar Nasarawa, jiya Laraba 19 ga Watan Disamba. Jami’in ‘Yan Sandan Kasar yace an kashe babban Sojan ne a wani kauye mai suna Tudu-Uku da ke hanyar Gitafa zuwa Keffi.

Jami’an ‘Yan Sandan sun nemi jama’a su bada hadin kai wajen gano wadanda su kayi wannan mummunan kisa a karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa a farkon makon nan kamar yadda Shugaban kasa ya ba su umarni.

An kashe Sojan ne bayan an harbe sa da bindiga tare da Direban sa. Har yanzu dai Abokin Mariagyi Alex Badeh, wanda su ke tare a lokacin yana hannun wadannan miyagun mutane inji Jami’an tsaro na kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel