Yadda Gwamnatin Buhari ta shirya kashe Tiriliyan 8.83 a shekara mai zuwa

Yadda Gwamnatin Buhari ta shirya kashe Tiriliyan 8.83 a shekara mai zuwa

A jiya Laraba 11 ga Watan Disamba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2019 mai zuwa gaban ‘Yan Majalisar Tarayyar Kasar. Legit Hausa ta kawo maku wasu muhimman abubuwa da ya dace ku sani game da kasafin na badi.

Yadda Gwamnatin Buhari ta shirya kashe Tiriliyan 8.83 a shekara mai zuwa

Gwamnatin Buhari ta yi kasafin Tiriliyan 8.83 kasa da abin da aka kasafta a bana
Source: Facebook

Ga kadan daga kanun kasafin na shekara mai zuwa:

1. Adadin kudin da za a kashe

Gwamnatin Tarayya ta ci burin batar da Naira Tiriliyan 8 da kuma Biliyan 800 da Naira Miliyan 300 da ‘yan kai a shekara mai zuwa. Wannan kudi za su fito daga harajin kasar ne da kuma kudin arzikin mai da bashi da sauran su.

2. Kudin manyan ayyuka

Daga cikin wannan kudi Naira Tiriliyan 8.83, ana sa rai Gwamnati ta kashe akalla Naira Tiriliyan 2 wajen gina abubuwan more rayuwa irin su tituna, layin dogo da gadoji da sauran su kamar yadda kundin kasafin na 2019 ya nuna.

KU KARANTA: Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari a Majalisa

3. Kudin da aka warewa albashi

Haka zalika, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ware sama da Naira Tiriliyan 4 wajen biyan albashi da kuma biyan bashin ma’aikata da sauran su. Sama da kashi 45% na kudin da za a samu a 2019 za su tafi ne wajen biyan albashi a Kasar.

4. Bashi

A cikin wannan kudi fiye da Tiriliyan 8, Gwamnatin Najeriya za ta cire sama da Naira Tiriliyan 2 wajen biyan bashin da ake bin kasar. Haka zalika kuma za a sake karbo wasu bashin da su ka haura Naira Tiriliyan 1.8 a shekara mai zuwa.

5. Kudin arzikin man fetur

Najeriya ta na sa ran samun abin da ya haura Tiriliyan 3.7 daga kasuwar man fetur a 2019. Gwamnati na sa rai ta samu kusan Tiriliyan 1.4 wajen kayan amfanin gona da ma’adanai da sauran su kamar yadda kasafin ya nuna.

6. Kudi daga hannun Barayi

Gwamnatin Tarayya ta kasafta wasu Biliyan 200 a gefe wanda ake tunani sun baro hannun Barayin Gwamnatin Kasar zuwa hannun hukuma. Kasafin kudin na badi ya kuma ware sama da Tiriliyan 1.25 da za a samu daga wasu haraji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel