Duk da kalubalan da muka fuskanta, Najeriya ta samu ci gaba ta kowace fuska - Buhari

Duk da kalubalan da muka fuskanta, Najeriya ta samu ci gaba ta kowace fuska - Buhari

- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya ce an samu kyakkyawan ci gaba a Najeriya a gwamnatin sa

- Jagoran Najeriya ya ce tsayuwa bisa aiki tukuru ta gwamnatin sa ya sanya Najeriya ke ci gaba da habaka

- Najeriya na kara yiwa matsin tattalin azriki nisan gaske a karkashin gwamnatin Buhari

Duk da manya da kananan kalubalai da kasar Najeriya ke ci gaba da fuskanta, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba ya bayyana cewa, hakan bai sanya an gaza samun ci gaba ta kowace fuska a fadin kasar nan.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya zayyana yadda juriya gami da jajircewar gwamnatin sa da kuma tsayuwa bisa aiki tukuru ya sanya kasar nan ta samu ci gaba da habakar tattalin arziki.

Yake cewa, jarumta gami da kwazon gwamnatinsa ta sanya Najeriya ke ci gaba da habaka bayan ta tsarkakewa da kuma tsamo ta daga matsi na tattalin arziki tsawon watanni 18 da suka gabata.

Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudin 2019 a zauren Majalisar tarayya

Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudin 2019 a zauren Majalisar tarayya
Source: UGC

Shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne yayin gabatar da kasafin kudin kasar nan na shekarar badi. Buhari a ranar Larabar da ta gabata ya gabatar da kasafin kimanin Naira Tiriliyan 8.83 a zauren majalisar dokoki ta tarayya da ke babban birnin kasar nan na Abuja.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nemi hukumomin tsaro su bankado makasan Alex Badeh

Jagoran kasar ya kuma bayyana cewa, sabanin yadda 'yan adawa da soki burutsu ke ikirari, gwamnatin sa ta yi bajintar gaske na samar da ci gaba fannikan noma, gine-gine na ci gaban kasa da kuma inganta jin dadi da kuma zamantakewar al'umma.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanatan Shiyyar Kaduna ta Tsakiya majalisar Dattawa, Shehu Sani, ya yi tsokaci dangane da ihun da 'yan Majalisar dokoki ta tarayya suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayin gabatar da kasafin kudin kasar nan na 2019 a jiya Laraba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel