Zamu amince da Jerry Gana a matsayin dan takarar shugaban kasa - SDP

Zamu amince da Jerry Gana a matsayin dan takarar shugaban kasa - SDP

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta ce ta samu umurni daga babban kotun tarayya na amincewa da Farfesa Jerry Gana a matsayin dan takarar shugbacin kasar ta a babban zaben 2019.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Abdul Isiaq ne ya bayyana hakan a yayin da ya tarbi Mr Gana da ya kai masa ziyarar ban girma a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja a ranar Laraba.

A ranar Juma'a da ta gabata ne Kotun tarayya da ke Maitama ta yanke hukuncin cewa tsohon ministan sadarwa, Mr Jerry Gana ne dan takarar shugabancin kasa na ainihi na jam'iyyar na SDP a babban zaben 2019.

A baya jam'iyyar ta zabi tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke a matsayin dan takarar ta a babban zaben na 2019.

Zamu amince da Jerry Gana a matsayin dan takarar shugaban kasa - SDP

Zamu amince da Jerry Gana a matsayin dan takarar shugaban kasa - SDP
Source: Depositphotos

Jam'iyyar ta zabi Mr Duke a matsayin dan takarar ta ne bayan ya samu kuri'u 812 a zaben fidda gwani yayin da Jerry Gana ya samu kuri'u 611.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Sai dai, Gana ya garzaya kotu inda ya nemi a bashi takarar shugabancin kasar saboda tsarin karba-karba da ke cikin kundin tsarin jam'iyyar.

A hukuncin da ya zartas, mai shari'a Hussein Baba-Yusuf ya ce dole ne dukkan mambobin jam'iyyar suyi biyaya ga dokokin da ke cikin kundin tsarin jam'iyyar.

Ya ce tsarin karba-karba da ke cikin kundin tsarin jam'iyyar ya ce ba zai yiwa shiugaban jam'iyya da dan takarar shugabancin kasa su fito daga yanki guda ba.

Mr Isiaq ya ce jam'iyyar za tayi biyaya ga umurnin kotu.

"Wannan jam'iyyar kamar yadda ku ka sani jam'iyya ce mai biyaya ga doka hakan yasa duk abinda kotu ta zartas za muyi biyaya ga hukuncin." inji shi.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa ya ce jam'iyyar za ta yi duk abinda ya dace domin amincewa da bukatun Mr Gana domin ya samu damar kaddamar da yakin neman zabensa.

A baya, Mr Gana ya bukaci jam'iyyar ta cika fom din takararsa ta mika wa INEC kamar yadda kotu ta bayar da umurni. Gana ya ce zai sanar da al'umma tsarinsa na wasu muhimman abubuwa 5 da ya ke son aiwatar wa a Najeriya da zarar jam'iyyar ta amince da takararsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel