Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

- Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya yi tsokaci kan ihun da 'yan majalisa suka rika yi yayin gudanar da kasafin kudin 2018

- Shehu Sani ya bayyana cewa abin takaici ne yadda 'yan majalisa na APC da takwarorinsu na jam'iyyun adawa suka rika hayaniya

- Ya ce bangare guda akwai 'yan korar Buhari da ke jinjina masa ko da bai aikata wani abin azo a gani ba sannan akwai 'yan adawa marasa girmama na gaba da su tare da kushe duk wani abu da shugaban kasar ya yi

Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi
Source: Depositphotos

Dan majalisar dattawa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Shugaba Muhammadu Buhari a zauren majalisar tarayya yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

A yayin da shugaban kasar ke gabatar da kasafin kudin ga hadakar majalisar wakilai da na dattawa a yau Laraba, 'yan majlisun na jam'iyyar APC mai mulki da na jam'iyyun adawa sun rika ihu a yayin da shugaban kasar ke gabatar da kasafin kudin.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

A lokacin da shugaban kasar ke lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu, mambobin jam'iyyar adawa ta PDP sun rika masa ihun nuna rashin amincewa sannan takwarorinsu na APC suka rika masa jinjina.

Hayaniyar da 'yan majalisar suka rika yi ta baci har sai da shugaban kasar ya janyo hankalinsu da cewa duniya na kallon abinda suke yi kuma za su kunyata Najeriya idan ba su bari ba.

A tsokacin da ya yi kan rashin natsuwar da 'yan majalisar suka nuna, Sanata Shehu Sani ya nuna takaicinsa kan yadda 'yan majalisar suka rika hayaniya yayin da shugaban kasar ke gabatar da kasafin kudin.

Ya ce: "A yayin gabatar da kasafin kudin zauren majalisar ya zama kamar dandali ne na shirme, a bangare daya akwai 'yan kora da zuga da ke neman shugaban kasa ya san da zamansu wadanda ke jinjina masa ko da ya kurba ruwa ne, a dayen bangaren kuma akwai tawagar marasa ganin girman nagaba da su da ke kokarin yin tawayye ta kowane hali."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel