Ku daina bawa 'yan sanda bashi - Kwamishinan 'yan sanda ya gargadi 'yan kasuwa

Ku daina bawa 'yan sanda bashi - Kwamishinan 'yan sanda ya gargadi 'yan kasuwa

- Fafowora Bolaji, kwamishna 'yan sandan jihar Kwara, ya shawarci jama'ar Jimba Oja da su guji sayar da kayansu ga jami'an 'yan sanda a kan bashi

- Kwamishnan ya ce bawa jama'ar wannan shawara ya zama domin gudun fadawa cikin mawuyacin hali yayin da aka yiwa jami'in da suka bawa bashi canjin wurin aiki

- Kazalika, kwamishinan ya mika godiya ga kamfanin da ya gina ofishin 'yan sandan tare da basu tabbacin cewar za ai amfani da shi wajen tabbatar da tsaro a yankin

Kwamishna 'yan sandan jihar Kwara, Fafowora Bolaji, ya shawarci jama'ar Jimba Oja da su guji sayar da kayansu ga jami'an 'yan sanda a kan bashi.

Bolaji ya ce bawa jama'ar wannan shawara ya zama domin gudun fadawa cikin mawuyacin hali yayin da aka yiwa jami'in da suka bawa bashi canjin wurin aiki.

Ya bayar da shawarar ne ranar Lahadi yayin taron bikin bude karamin ofishin 'yan sanda a Kamwire dake Jimba Oja, da kamfanin KAM suka gina.

Ku daina bawa 'yan sanda bashi - Kwamishinan 'yan sanda ya gargadi 'yan kasuwa

'yan sanda
Source: Depositphotos

"Kar ku sake ku sayar da kayanku bashi ga jami'an 'yan sanda saboda za a iya yi masa canjin wurin aiki a kowanne lokaci," a cewar Bolaji.

Kazalika, kwamishinan ya mika godiya ga kamfanin da ya gina ofishin 'yan sandan tare da yi masu albishir din cewar zai tabbatar hukamar 'yan sanda reshen jihar Kwara tayi amfani da ofishn domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'ummar yankin.

A nasa jawabin, Dakta Kamaruddeen Yusuf, shugaban kungiyar masu masana'antu a jihar Kwara da Kogi, ya bayyana shigar jama'a harkokin tabbatar da tsaro da abu mai matukar muhimmanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel