Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba

Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba

Sama da kungiyoyi 469 da ke goyon bayan Atiku, suka zargi ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa Atiku, APCO, da mayar da su saniyar ware a harkokin siyasar jam'iyyar ta PDP, inda kuma suka yi barazanar sauya akalarsu ma damar ba ayiwa tufkar hanci ba.

Akalla kungiyoyin siyasa 469 ne dake nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, suka yi barazanar ballewa daga tafiyar ma damar ba a yiwa tufka hanci ba, kan yadda aka mayar da su saniyar ware a tafiyar.

Kungiyoyin wadanda suka hadu a karkashin inuwar kungiya daya mai suna APCO Support Group, sun gargadi shuwagabannin jam'iyyar PDP na kasa da su farka daga baccin da suke yi, tare da gujewa durkusar da dan takarar shugaban kasar, Atiku Abubakar, kamar yadda suka yiwa Goodluck Jonathan a 2015.

KARANTA WANNAN: Jose Mourinho ya maida martani kan korarsa daga Man United, ya caccaki Ed Woodward

Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba

Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin, Mr. Amb. Enobong Iyang, wanda aka fi sani da Don P, ya yi barazanar janye goyon bayan da suke yiwa Atiku ma damar ba a dauki matakan magance wannan matsala tasu ba.

Kungiyar na zargin shuwagabannin ofishin yakin Atiku, na nuna halin ko in kula ga su, da kuma rashin nuna godiyarsu akan duk irin ayyukan da suke gudanarwa, la'akari da cewa ba biyansu ake ba, sune ke cirewa daga aljihunansu, don nuna kishin Atiku da bukatar sauyin gwamnati.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel