Saura kiris: Wani tsohon gwamnan PDP a arewa ya kammala shirin komawa APC

Saura kiris: Wani tsohon gwamnan PDP a arewa ya kammala shirin komawa APC

A yadda al'amurra ke tafiya, labarin da ke iso mana yana nuni ne da cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi a karkashin tutar jam'iyyar PDP kuma wanda ya shugabanci jam'iyyar a baya, Alhaji Adamu Mu'azu zai koma ja'iyya mai mulki ta APC cikin yan kwanakin nan kadan masu zuwa.

Kamar yadda muka samu dai, fitaccen dan siyasar da aka shedi cewar ya iya siddabaru da dabarun neman jama'a domin cin zabe, tuni ya kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata na komawar ta sa.

Saura kiris: Wani tsohon gwamnan PDP a arewa ya kammala shirin komawa APC

Saura kiris: Wani tsohon gwamnan PDP a arewa ya kammala shirin komawa APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Karon farko Buhari yayi magana game da 'yan ASUU

Legit.ng Hausa ta samu cewa da marcen ranar Laraba ne ma dai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya sa labule da tsohon gwamnan a fadar shugaban kasa a wani matakin da ake kallon tamkar na karshe na sauya shekar ta sa.

Haka ma dai masu sharhi kan al'amurran yau da kullum sun bayyana cewa halartar daurin auren diyar sa da mataimakin shugaban kasar yayi a makon da ya gabata a jihar Bauchi duk yana cikin shirye-shiryen zawarcin sa da APC din ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel