Atiku ya yiwa Buhari gori a kan karuwar marasa aiki a Najeriya

Atiku ya yiwa Buhari gori a kan karuwar marasa aiki a Najeriya

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kara ragargazar shugaba Buhari a kan abinda ya kira cuwa-cuwa a alkaluman rashin aikin da gwamnatin tarayya ta fitar.

Da yake in raddi a kan rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a kan rashin aiki, Atiku ya ce mutane miliyan 20.93 ne suka rasa aiki a karkashin gwamnatin APC.

A jawabin na Atiku da Paul Ibe, mai taimaka masa a bangaren yada labarai ya fitar, ya zargi shugaba Buhari da juya shugaban hukumar NBS, Dakta Yemi Kale, domin fitar da alkaluman da gwamnati ke so.

Jawabin ya ce, "babban abun damuwa ne a ce mutane miliyan 20.93 sun rasa aiki a karkashin gwamnatin Buhari. Wadannan alkaluma ne na hukumar kididdiga dake karkashin ikon shugaban kasa.

Atiku ya yiwa Buhari gori a kan karuwar marasa aiki a Najeriya

Atiku da Buhari
Source: Depositphotos

"Hakan na nufin kenan adadin 'yan Najeriy marasa aiki kacal ya ninka adadin jama'ar kasar Benin sau biyu.

"Najeriya ba zata cigaba da zama a haka ba, musamman ganin yadda wannan gwamnatin ta mayar da hankali wajen zargin wasu da duk wata gazawarta sabanin neman hanyoyin da zata magance matsalolin da kasa da 'yan kasa ke ciki.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka yiwa Buhari ihu - 'Yan majalisar PDP

"Muna kira ga 'yan Najeriya su san cewar shugaban da ya kasa kawowa kasuwancinsa cigaba, ba zai iya kirkirar aiyuka ga jama'a ba balle su ma su yi arziki, saboda mutum ba zai iya bayar da abinda bashi da shi."

Kazalika jawabin ya yi godiya ga babban darektan hukumar NBS bisa kokarinsa na fitar da alkaluman da suka bayyana gaskiyar yanayin rashin aiki da ake ciki a kasa ba tare da tsoro ko shakkar shugaban kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel