APC ta dora alhakin yiwa Shugaba Buhari ihu ga Saraki da Dogara

APC ta dora alhakin yiwa Shugaba Buhari ihu ga Saraki da Dogara

Jam'iyya mai mulki a matakin tarayya a Najeriya ta APC ta ce 'yan Najeriya da ma sauran al'ummar duniya su fito suyi Allah-wadai da halin rashin dattakun da 'yan majalisar tarayya suka nunawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yau lokacin da yake gabatar masu da kasafin kudin 2019.

Haka zalika jam'iyyar a cikin sanarwar da suka fitar dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'ar ta ya fitar, yace su dukkan abun da ya faru sun dora alhakin hakan ne ga shugabannin zaurukan majalisar biyu watau Sanata Bukola Saraki da kuma Honorabul Yakubu Dogara.

APC ta dora alhakin yiwa Shugaba Buhari ihu ga Saraki da Dogara

APC ta dora alhakin yiwa Shugaba Buhari ihu ga Saraki da Dogara
Source: UGC

KU KARANTA: Muhimman batutuwa 5 da Buhari yayi magana kan su a majalisa

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cewar APC din, inda shugabannin sun tsawata ma 'yan jam'iyyar ta su da hakan bai faru ba amma sai suka zura masu ido wanda hakan ke nuni da cewa akwai sa hannun su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha ihu a majalisar dokoki yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.

Shugaban ya sha tafi daga magoya bayansa amma 'yan adawa sai ihu suke suna cewa 'karya ne' yayin da yake jawabi kan nasarorin gwamnatinsa a majalisar da jam'iyyar PDP ke jagoranta wasu kuwa 'yan majalisar suna yi masa tafi tare da furta kalaman karfafa masa guiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel