Dalilin da yasa muka yiwa Buhari ihu - 'Yan majalisar PDP

Dalilin da yasa muka yiwa Buhari ihu - 'Yan majalisar PDP

Daya daga cikin mambobin majalisar wakilai 'yan jam'iyyar PDP ya bayyana cewar sun yiwa shugaba Buhari ihu ne domin nuna rashin jin dadinsu bisa yadda gwamnatin tarayya ta gaza yin aiki da kasafin kudin shekarar 2018 kamar yadda ta gabatar.

A yau, Laraba, ne wasu mambobin majalisar wakilai suka yiwa shugaba Buhari ihu yayin da ya isa zauren majalisar domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Da shigar Shugaba Buhari zauren majalisar sai wasu mambobi suka kaure da ihun "noooo", "noooo" tare da yin ihun "karyane", "karyane" lokacin da Buhari ya fara zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Dalilin da yasa muka yiwa Buhari ihu - 'Yan majalisar PDP

Dalilin da yasa muka yiwa Buhari ihu - 'Yan majalisar PDP
Source: UGC

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala gabatar da kasafin, shugaban wata kungiyar 'yan majalisar tarayya Jam'iyyar PDP, Chukwuma Onyema, ya bayyana rashin jin dadin 'yan majalisar a kan yadda bangaren zartarwa ke nuna son a kai wajen zabar aiyukan da zata kaddamar daga cikin wadanda ta gabatar a kasafinta na shekarar 2018.

Kazalika, ya bayyana cewar hatta yajin aikin da ma'aikatan majalisar ke yi na da alaka da rashin kaddamar da kasafin kudin shekarar 2018.

Tunda safe ne legit.ng ta sanar daku cewar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ministoci da hadiman shugaba Buhari masu yawa sun isa zauren majalisa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Osinbajo da hadiman sun isa zauren majalisar ne da misalin karfe 11:50 na safe, yayin da ake sa ran shugaba Buhari zai iso zauren majalisar da misalin karfe 12:00 na rana.

Sai dai wasu rahotannin da suka iso wa legit.ng sun bayyana cewar sanatoci sun fara zaman majalisa bayan gajiya da jiran karasowar shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel