Da duminsa: An damke matar kwamandan Boko Haram, Mamman Nur ta kawo harin kunar bakin wake

Da duminsa: An damke matar kwamandan Boko Haram, Mamman Nur ta kawo harin kunar bakin wake

Kwamandan hukumar NSCDC na jihar Borno, Abdullahi Ibrahim, ya bayyana cewa daya daga cikin matan yan Boko Haram biyu da suka damke matar shugaban wani bangaren Boko Haram ce, Mamman Nur.

Yar yarinyar mai suna, Fatima Kabir, ta shiga hannu ne tare da wata mata mai suna, Amina Salihu, a tashar motar Borno Express. Manufarsu shine kai harin kunar bakin wake cikin garin Maidugri, sun bayyana yayin bincike.

Mista Ibrahim ya bayyana cewa wani jami'in NSCDC da ya tattauna da su ya wayance musu a matsayin wani kamammen dan Boko Haram.

Ya laburta wannan bayani ne a taron kaddamar da wasu kayan aiki da gwamnatin kasar Amurka ta baiwa Najeriya a ranan Laraba, 19 ga watan Disamba, a garin maiduguri.

KU KARANTA: Rikici ya barke a majalisar dokokin tarayya, yan majalisa na kokarin cin mutuncin Buhari

A jawabinsa: "Sama da yan Boko Haram 40 sun mika wuya ga hukumar. Mun mikasu ga hukumar soji domin sauya tunaninsu. Mun samu nasarar gamsar dasgu cewa su mika makamansu kuma su amince a sauya musu tunani a damar da gwamnati ta basu."

"A zaman da sukayi a nan, sunce suna Sallah sau biyar a kowace ranan sabanin lokacin da suka daji suna yaki,"

Mr Ibrahim ya karashe da cewa akalla jami'an hukumar 1,000 aka tura yakin Boko Haram a yankin Arewa maso gabas, tare da wasu abokan sikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel