Muhimman batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo wajen gabatar da kasafin kudin 2019

Muhimman batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo wajen gabatar da kasafin kudin 2019

- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.83 ga majalisar dokokin kasar.

- An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana.

- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.83 ga majalisar dokokin kasar.a daya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.

Muhimman batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo wajen gabatar da kasafin kudin 2019

Muhimman batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo wajen gabatar da kasafin kudin 2019
Source: UGC

KU KARANTA: Karon farko, Buhari yayi magana game da 'yan ASUU

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan an samu raguwar hauhawan farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo ma sa sowa da ihu daga bangaren 'yan adawa a zauren majalisar.

Ga dai wasu abubuwan da ya fada nan mun zakulo maku:

1. Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki.

2. Hauhawan farashin kayayyaki ya ragu daga kashi 18.17 a Janairun 2017 zuwa kashi 11.28 a Nuwamban banaKudin ajiyarmu ya karu daga dala bilian $28.57 a Mayun 2015 zuwa dala biliyan $42.92 a tsakiyar Disemban 2018.

3. Mun yi kokari wajen magance matsalar tsaro a arewa maso gabas da rikicin kabilanci a wasu wurare.

4. Mun samu nasara a yaki da cin hanci da rashawaMun hana shigo da shinkafa daga wajeMun samu ci gaba sosai wajen ayyukan ci gaba.

5. Mun yi kokarin kammala ayyukan da muka samu maimakon kirkirar wasu sabbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel