Jose Mourinho ya maida martani kan korarsa daga Man United, ya caccaki Ed Woodward

Jose Mourinho ya maida martani kan korarsa daga Man United, ya caccaki Ed Woodward

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu daga kafar watsa labarai ta kasar Burtaniya, 'The Mirror', na nuni da cewa Eladio Parames, mai magana da yawun Jose Mourinho, ya caccaki Ed Woodward, kan korar da Man United ta yiwa mai gidan nasa.

Babban mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na kasa da kasa, Jose Mourinho, wanda kungiyar kwalon kafa ta Manchester United ta koreshi daga shugabantarta a ranar Talata, ya maida martani kan wannan kora da hali, tare da caccakar Ed Woodward.

Mai magana da yawun Jose Mourinho, Eladio Parames, shi ne ya yi wannan caccakar a madadin mai gidan nasa.

Akwai doguwa kuma kyakkyawar alaka tsakanin Parames da tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar ta Manchester United, wanda yayi amfani da shafinsa na wata jaridar wasanni ta kasar Fotugal wajen kare mai gidan nasa.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Ahmad Muazu ya saka labule da Osinbajo a Abuja

Jose Mourinho ya maida martani kan korarsa daga Man United, ya caccaki Ed Woodward

Jose Mourinho ya maida martani kan korarsa daga Man United, ya caccaki Ed Woodward
Source: Getty Images

A ranar safiyar ranar Talata, bayan wata ganawar mintuna 44 tsakanin Mourinho da Woodward a Carrington, kungiyar kwallon kafar ta Man United ta sanar da korar sa daga mai horas da 'yan wasanta.

Wannan mataki na kungiyar kwallon kafar na korar tsohon shugaban kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Real Madrid, ya biyo bayan awanni 48 bayan da United ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 3-1.

Wannan kashi da United ta sha a filin wasa na Anfied, ya maido da kungiyar kwallon kafar zuwa matsayi na 6 da maki 19, wacce ta dawo kasan masu rike da kambun kofin Firimiya, kumamanyan abokan hamayyarsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel