Tun 1960 Najeriya bata taba dace da shugabannin masu nagarta kamar ni da Obi ba - Atiku

Tun 1960 Najeriya bata taba dace da shugabannin masu nagarta kamar ni da Obi ba - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya ce shi da mataimakinsa Peter Obi za su gabatar da salon shugabancin da Najeriya ba ta taba gani ba

- Atiku ya ce shi da Obi dukkansu kwararu ne a aikin gwamnati da kuma kasuwanci saboda hakan sune za su iya ceto Najeriya daga halin da ta shiga

- Tsohon shugaban kasar ya gargadi al'umma kada suyi kuskuren sake zaben jam'iyyar APC saboda ita ta jefa kasar cikin wahala

A yau, Laraba ne dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce shi da mataimakinsa Peter Obi za su nuna wa 'yan Najeriya sabon salon mulkin da kasar ba ta taba gani ba tun samun 'yanci a shekarar 1960.

A jawabin da Atiku ya yi wurin taron jin ra'ayin mutane da jagororin 'yan kasuwa a garin Aba in jihar Abia, ya ce gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress ce ta janyo tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Tun 1960 Najeriya bata taba dace da shugabannin masu nagarta kamar ni da Obi ba - Atiku

Tun 1960 Najeriya bata taba dace da shugabannin masu nagarta kamar ni da Obi ba - Atiku
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Buhari ya ki amincewa da kudirorin kafa wasu hukumomi biyu a fanin sufuri

A cewar dan takarar na jam'iyyar PDP, Najeriya ba zata cigaba da rayuwa a irin wannan halin da matasa miliyan 50 ba su da ayyukan yi.

Ya ce, "Shi yasa ake samun tashe-tashen hankula. Kafin mutum ya yi kasuwanci, yana bukatar tsaro. Idan ba haka ba mutum ba zai iya fitowa daga gidansa ya tafi wurin sana'arsa ba.

"Ni da abokin takara na Peter Obi kwararu ne a aikin gwamnati da kasuwanci. Bana tunanin an taba samun irin wannan shugabancin a Najeriya tun lokacin da kasar ta samu 'yanci. Idan shakka kun san abinda ya dace kuyi, ku gwada mu ku gani."

Atiku ya lissafo kamfanoni daban-daban da ya ke yi kamar kamfanin sarrafa ababen sha, kiwo, sayar da abinci, sufuri, gidajen talabijin da rediyo da sauransu.

Ya ce jam'iyyar PDP ce tayi kokarin magance matsalolin da 'yan kasuwar kasar nan ke fuskanta kuma a yanzu ga wata dama ta samu da al'umma za su sake zaben jam'iyyar. Ya yi kira da al'umma kada su sake kuskuren mayar da APC a kan mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel