Paris Club: Fayose ya barnatar da Biliyan 18 a Jihar Ekiti – inji Fayemi

Paris Club: Fayose ya barnatar da Biliyan 18 a Jihar Ekiti – inji Fayemi

Gwamnan Jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya bayyana cewa Ayodele Peter Fayose ya barnatar da Naira Biliyan 18 da Gwamnatin Tarayya ta aikowa Jihar kwanaki daga cikin bashin da ta ke bi na Paris Club.

Paris Club: Fayose ya barnatar da Biliyan 18 a Jihar Ekiti – inji Fayemi

Gwamna Fayemi yace Fayose ya bar Jihar Ekiti da aiki
Source: Depositphotos

Kayode Fayemi ya bayyana cewa Ayo Fayose bai biya bashin albashin da Ma’aikatan Jihar Ekiti su ke bi ba duk da cewa ya karbi kudi har Naira Biliyan 18 daga cikin Biliyan 21.5 da Jihar Ekiti ta ke bin Gwamnatin Tarayya a baya.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne a Garin Ado Ekiti inda ya karyata radi-radin cewa ya karbi kudi daga hannun Shugaba Buhari. Fayemi ya tabbatar da cewa bai karbi wasu Biliyan 30 na gyaran tituna a wajen Gwamnatin Tarayya ba.

KU KARANTA: Yadda Dogara ya roki 'Yan majalisa game da tozarta Buhari

Gwamnan yace ya ki nada mukamai ne a dalilin bashin da yayi wa Jihar Ekiti katutu saboda barnar kudin da Gwamnatin Fayose tayi. Fayemi yace yanzu mutanen Jihar Ekiti sun gane irin barnar da PDP tayi a Jihar Ekiti a shekaru 4.

Gwamnan na Ekiti yace daga cikin Biliyan 18 da Shugaba Buhari ya aikowa Jihar Ekiti, Biliyan 3.5 kacal ya rage a asusun Gwamnatin Jihar. Kayode Fayemi yace kudin da Magajin sa Ayo Fayose ya rage, bai isa a biya albashin wata guda ba.

Sai dai wani Hadimin tsohon Gwamna Ayo Fayose, Lere Olayinka, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta bada sharuda kafin ta aikowa Jihar Ekiti kudin na Paris Club. Fayose yace bashin da Fayemi a 2014 ya bari ya sa kudin su ka kare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel