Shugaba Buhari ya nemi hukumomin tsaro su bankado makasan Alex Badeh

Shugaba Buhari ya nemi hukumomin tsaro su bankado makasan Alex Badeh

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya janjanta kwarai da aniyya dangane da kisan gillar tsohon shugaban hafsin dakarun sojin Najeriya, Air Chief Marshal Alex Badeh.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a Yammacin jiya na Talata, 'yan bindiga dadi suka bindige tsohon sojin yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga gona a kauyen Gitata da ke karkashin karamar hukumar Keffi ta Nasarawa.

Lamari dai ya janyo cecekuce a fadin kasar nan, yayin da wasu ke ganin barayi ke da hannu cikin wannan muguwar aika-aika, wasu na hasashen 'yan Boko Haram ne suka yi ma sa kwanton bauna. Wa su daga cikin 'yan uwansa na tsammanin hannun gwamnati cikin wannan lamari.

Air Chief Marshal Alex Badeh.

Air Chief Marshal Alex Badeh.
Source: Facebook

Shugaba Buhari ya nemi hukumomin tsaro su bankado makasan Alex Badeh

Shugaba Buhari ya nemi hukumomin tsaro su bankado makasan Alex Badeh
Source: Facebook

Cikin wata sanarwa da sanadin kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shugaban kasa Buhari ya janjanta tare da mika sakon gaisuwar sa ta ta'aziyya ga iyalai, 'yan uwa, abokanan aiki da kuma al'ummar jihar Adamawa dangane da wannan babban rashi da aka yi a kasar nan.

Shugaban kasa Buhari ya bayar da umarni ga dukkanin hukumomin tsaro na kasar nan, akan mikewarsu tsaye wajen bankado miyagun da ke da hannu cikin wannan muguwar ta'ada domin su fuskanci fushin doka daidai da abin da suka aikata.

KARANTA KUMA: Hatsari ya salwantar rayukan Abokanai da Waliyan Ango 9 a jihar Nasarawa

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya kuma mika kokon bararsa ga Mai Duka akan ya jikan Marigayi Alex Badeh tare da bai wa hakurin jure wannan babban rashi.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai yiwuwar iyalan marigayi Alex Badeh da suka shafe kimanin shekaru uku a kasar Amurka ba za su samu damar halartar jana'izar sa ba sakamakon fargabar takunkumin da hukumar tsaro ta DSS ta sanya a kansu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel