Jerin sunaye: Hukumar soji ta yiwa Janar 5 ritaya

Jerin sunaye: Hukumar soji ta yiwa Janar 5 ritaya

A jiya, Talata, ne hukumar soji ta yiwa Manjo Janar biyu da Birgediya Janar uku ritaya a rukunin likitoci na rundunar soji.

Janar din 5 da hukumar soji ta yiwa ritaya sune; Manjo Janar Abimbola Amusu, Manjo Janar Patrick Falola, Birgediya janar Folorunsho Jegede, Birgediya janar O. Akinyode da Birgediya Janar M. Robbinson.

Manyan jami'an rundunar soji sun halarci faretin ban kwana da aka shiryawa sojojin.

Jerin sunaye: Hukumar soji ta yiwa Janar 5 ritaya

Jerin sunaye: Hukumar soji ta yiwa Janar 5 ritaya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Daya daga cikin Janar din da suka yi ritaya, Amusu, ta ce sadaukarwar ta da taimakon ubangiji ya kai ta ga samun nasara a aikin soji.

Ta yiwa sojojin dake da ragowar lokaci a cikin aiki nasihar da su mayar da hankali a kan aiki muddin suna bukatar samun nasara a cikin rayuwar su ta aikin soja.

Kwamandan soji, Manjo Janar Joel Unnigbe, ce ta wakilci hafsan dakarun soji na kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel