'Yan sanda sun kama mutumin da ya lakadawa mahaifiyar matarsa duka

'Yan sanda sun kama mutumin da ya lakadawa mahaifiyar matarsa duka

'Yan sanda sun gurfanar da wani Seun Okwuyigbo mai shekaru 35 a gaban kotun majistare da ke zamanta a Ogudu na jihar Legas bisa zarginsa da yiwa mahaifiyarsa matarsa duka da ji mata rauni a idon ta.

Mai shigar da kara, Inspecta Lucky Ihiehie ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargi ya aikata laifin ne a gida mai lamba 7 Shifawa Street da ke Ikosi-Ketu a ranar 14 ga watan Dismbar wannan shekarar.

Ya ce wanda ake zargin ya yiwa surukansa, Tolani Bisiritu mai shekaru 65 duka a yayin da ta ke kokarin gano dalilin da yasa Okwuyigbo ya kulle diyarta da yaranta a wani daki ya hana su fita.

'Yan sanda sun kama mutumin da ya lakadawa mahaifiyar matarsa duka

'Yan sanda sun kama mutumin da ya lakadawa mahaifiyar matarsa duka
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Ihiehie ta ce laifin ya sabawa sashi na 173 na dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2015.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa idan laifin ta tabbata, ana iya daure mai laifin tsawon shekaru uku a gidan yari.

Bayan an karanto masa karar, Okwuyigbo ya musanta aikata laifin.

Shugaban kotun, Majistare E. Kubeinje ya bayar da belinsa a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su karbi belinsa.

Mr Kubeinje ya ce dole wanda za su karba belinsa su gabatar da takardun biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas kuma su kasance masu sana'a.

Alkalin ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel