Gwamnatin tarayya zata haramta shigowa da masara - Ministan noma

Gwamnatin tarayya zata haramta shigowa da masara - Ministan noma

- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce nan bada jimawa ba zata iya haramta shigowa da masara kasar la'akari da cewar masarar yanzu ta wadata

- Haka zalika, gwamnatin tarayyar ta ce zata yiwa cibiyar nazari da bincike kan harkokin noma ta kasa NARC garambawul kan gazawarta na gudanar da aiki yadda ya dace

- A hannu daya kuwa, majalisar wakilan tarayya ta bayyana bukatar janye kasafin kudin noma daga cikin kasafin da kasar ta saba gabatarwa kowacce shekara

Gwamnatin tarayya ta ce tana duba yiyuwar haramta shigowa da masara kasar, duba da cewa masarar ta wadata sakamakon noman da yayi albarka a daminar bana a kasar.

Ministan noma da bunkasa karkara, Chief Audu Ogbeh, ya bayyana hakan a wani taron da kwamitin noma na hadakar majalisun dokokin tarayyar kasar ya kai ziyara a ma'aikatar don duba yanayin gudanarwar ayyukanta, a Abuja.

Ogbeh ya kuma kalubalanci cibiyar nazari da bincike kan harkokin noma ta kasa (NARC) na gazawarta wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

KARANTA WANNAN: Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019

Gwamnatin tarayya zata haramta shigowa da masara - Ministan noma

Gwamnatin tarayya zata haramta shigowa da masara - Ministan noma
Source: Depositphotos

"Akwai bukatar sake fasalin nazari da bincike kan harkokin noma ta kasa (NARC) wacce ko kadan bata cimma ayyukanta kuma akwai karya dokokin gudanar da ayyukan gwamnati da ake zargin cibiyar da yi.

"Zamu fara daukar shawarar 'yan majalisu, kuma ya zama wajibi mu dauki mataki don yiwa tufkar hanci, kuma muna duba yiyuwar haramta shigowa da masara tunda dai yanzu ta wadata a kasar," a cewarsa.

A nashi bangare, shugaban kwamitin harkokin noma na majalisar tarayya, Hon. Tahir Monguno, ya kawo shawarar janye kasafin kudin noma daga cikin kasafin da aka sabayi na shekara shekara, yana mai cewa harkar noma wata abace mai amfani da lokaci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel