Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019

Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019

- Yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu gagarumar gudunmowar kudi har N1.2bn don bashi damar yin tazarce a 2019

- Kudaden zasu fito ne daga hannun kungiyar manoman da ke cin gajiyar shirin Anchor Borrowers, wadanda ke da mambobi a fadin kasar

- Manoman da suka kai milyan 12, sun ce yin karo karon 100 kowannensu zai taimakawa yakin zaben Buhari, kuma sunyi hakan don yaba masa kan shirin ABP

Yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu gagarumar gudunmowar kudi a wanan yammaci yayin da manoma miliyan 12 da suka ci gajiyar shirin tallafawa manoma na babban bankin Nigeria (CBN) mai taken Anchor Borrowers, suka shiryawa shugaban kasar wata liyafa a Abuja, tare da yin karo karon N100 kowanne don daukar nauyin yakin zabensa a 2019.

A cewar wani rahoton daga jaridar THISDAY, wannan karo karo zai hadawa shugaban kasar N1.2bn kuma kudaden zasu fito ne daga hannun kungiyar manoman da ke cin gajiyar shirin Anchor Borrowers, wadanda ke da mambobi a fadin kasar, musamman ma a shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Da yake bayyana taken nan na cewar yaba kyauta tukuici, daya daga cikin shuwagabannin manoman, wanda ya baukaci a sakaya sunansa, ya ce suna cike da jin dadin wannan shugabanci na Buhari kasancewar ya bunkasa wannan sana'a tasu ta noma.

KARANTA WANNAN: Dogara ya gabatarwa Buhari wata babbar bukata

Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019

Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019
Source: Depositphotos

"Baba Buhari ya kasance yana yi mana duk wani abu da shugaba ya kamata ya yiwa manoma, don haka muna ganin yin karo karon N100 kowannenmu zai taimaka sosai wajen nuna godiyarmu garesha" a cewarsa.

Babban bankin Nigeria (CBN) ya samar da wannan shiri na baiwa manoma rance na Anchor Borrowers Programme (ABP), sannan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara shirin a ranar 17 ga watan Nuwamba 2015.

Zuwa watan Ogustar 2018, akalla N150bn ne aka rabawa manoma karkashin wannan shiri na ABP.

Wannan yunkuri na kungiyar masu cin gajiyar shirin zai taimaka ainun wajen gudanar da harkokin yakin zaben tshugaban kasa Buhari a karo na biyu, musaman ganin yadda kungiyar tayi yunkurin saiwa shugaban kasar fom na tsayawa takara a lokacin zaben fitar da gwani.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel