Fadar shugaban kasa ta shirya gabatar da mafi karancin albashi ga majalisar dokoki - Buhari

Fadar shugaban kasa ta shirya gabatar da mafi karancin albashi ga majalisar dokoki - Buhari

- Shugaba Buhari yace bada jimawa ba za’a tura dokar albashi mafi karanci ga majalisar dokoki domin gabatar da shi

- Buhari ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da kasafin kudin 2019 a zauren majalisun kasar guda biyu

- Ya bayar da tabbacin cewa ya jajirce wajen ganin ya magance lamarin mafi karancin albashi, cewa ya yi umurni ga a kafa wani kwamitin fasaha domin duba tsarin da za’a bi wajen aiwatar da manufar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bada jimawa ba za’a tura dokar albashi mafi karanci ga majalisar dokoki domin gabatar da shi.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Disamba yayin gabatar da kasafin kudin 2019 a zauren majalisun kasar guda biyu.

Ya bayar da tabbacin cewa ya jajirce wajen ganin ya magance lamarin mafi karancin albashi, cewa ya yi umurni ga a kafa wani kwamitin fasaha domin duba tsarin da za’a bi wajen aiwatar da manufar.

Fadar shugaban kasa ta shirya gabatar da mafi karancin albashi ga majalisar dokoki - Buhari

Fadar shugaban kasa ta shirya gabatar da mafi karancin albashi ga majalisar dokoki - Buhari
Source: UGC

“Domin guje ma wani tsari na rikici a gwamnatin tarayya da jihohi, yana da matukar muhimmanci bin tsarin da zai tabatar da manufar mai kai ga kari a yanayin rancen kudi ba.

“Nima zan kafa wani babban kwamitin fasaha domin bayar da shawara kan yadda za’a kara mafi karancin albashin ba tare da an samu Karin rancen kudi ba."

KU KARANTA KUMA: Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Buhari yace kwamitin zai bayar da shawarwari kan manufar sabon karancin albashi.

A cewarsa wannan yunkuri na daga cikin kokarin tabbatar da cewa gabatar da lamarin bai haifar da rasa ayyukan yin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel