Gabatar da kasafin kudin 2019: Yadda Dogara ya roki yan majalisa kan kada su tozarta Buhari

Gabatar da kasafin kudin 2019: Yadda Dogara ya roki yan majalisa kan kada su tozarta Buhari

- Yakubu Dogara ya roki yan majalisa a farfajiyarsa da kada su tozarta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hanyar yin zanga-zanga a lokacin gabatar da kasafin kudin 2019

- Kakakin majalisar ya gana da fusatattun yan majalisan, inda ya bukaci da su jingine zanga-zangar da suka shirya yiwa yi

- Wata majiya tace bayan rokon, sai wasu fusatattn yan majalisa suka janye sannan suka gabatar da kwalayensu ga Kawu Sumaila

Rahotanni sun kawo cewa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya roki yan majalisa a farfajiyarsa da kada su tozarta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hanyar yin zanga-zanga a lokacin gabatar da kasafin kudin 2019.

Wasu majiyoyi sun fada ma jaridar The Cable cewa kakakin majalisar ya gana da fusatattun yan majalisan, inda ya bukaci da su jingine zanga-zangar da suka shirya yiwa Buhari yayinda yake gabatar da kasafin kudin.

Gabatar da kasafin kudin 2019: Yadda Dogara ya roki yan majalisa kan kada su tozarta Buhari

Gabatar da kasafin kudin 2019: Yadda Dogara ya roki yan majalisa kan kada su tozarta Buhari
Source: Twitter

Wata majiya tace bayan rokon, sai wasu fusatattn yan majalisa suka janye sannan suka gabatar da kwalayensu ga Kawu Sumaila, babban hadimin shugaban kasar a kan harkokin majalisar wakilai.

“Duk a cike suke, kun san mafi akasarinsu basu samu tikitin komawa majalisar ba shiyasa suka so yin zanga-zanga. Wannan dalilin ne yasa aka samu jinkiri, kamata yayi ace an fara zaman da karfe 12:00 na rana.

KU KARANTA KUMA: Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

“Sun fara ajiye kwalayen zanga-zangansu ga Kawu Sumaila, cewar majiyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel