Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu

Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu

- Suna Amurka tun 2016 bayan da aka kama shi da tuhumar handamar kudin makamai

- Makusancin iyalin yace ba lallai su iya zuwa ba

- Watakil in suka shigo Najeriya basu iya fita

Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu

Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu
Source: UGC

Rahotanni dake fitowa daga iyalan Alex Badeh, wadanda ke can a Amurka kusan shekaru uku, tun bayann hawan mulkin Janar Buhari, sun nuna ba lallai su iya shigowa Najeriya domin makoki ko Jana'izar Janar din ba.

Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu

Iyalan Alex Badeh na iya rasa jana'izarsa saboda takunkumin da DSS suka sanya musu
Source: Facebook

A cewar makusancin iyalin, wanda ya zanta dasu a waya, yace suna shakkun lamarin da ma ya kai ga halakar mahaiin nasu a Najeriya, balle har su iya shigowa, kuma su fita lafiya ba'a kwace fasfunansu ba.

An dai tuhumi shugaban hafsoshin na tsaro da azurta kansa a mulkin PDP, ana tsaka da yaki da Boko Haram, kuma shima ya rasa iyalansa na nesa daga maharan, wadanda suka kwace gidansa a Mubi suka mayar shalkwatarsu ta tafka tsiya.

DUBA WANNAN: Bayan da Diamond ya zamo Access Bank, hannayenn jari sun hau

An bindige Janar din na soji ne a daren jiya, bayan ya dawo daga gona, lamari da ake gani ko dai barayi ne dake tsammanin ko kudi ya binne a gonar, ko kuma Boko Haram ne suka yi masa kwanton bauta. Wasu daga iyalinsa ma na zargin gwamnati ne.

Gwamnatin dai ta dade da sanya wa da yawa daga manyan kasar nan takunkumi, son kada su tsere ba'a gama shari'ar ko dawo da kudin da ake zarginsu da handame wa ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel