Buhari ya ki amincewa da kudirorin kafa wasu hukumomi biyu a fanin sufuri

Buhari ya ki amincewa da kudirorin kafa wasu hukumomi biyu a fanin sufuri

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki saka hannu kan wasu kudurori guda biyu na kafa wasu hukumomi a fannin sufuri saboda a cewarsa mafi yawancin ayyukan da ake sabbin hukumomin za suyi maimaici ne kawai domin a halin yanzu akwai hukumomi ko ma'aikatu da ke wadannan ayyukan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki saka hannu a akan wasu kudurori guda biyu, Kudirin hukumar sufuri na 2018 da kuma kudirin hukumar kula da tittunan tarayya na shekarar 2018.

Shugaban kasar ya bayyana rashin amincewarsa da kudirorin ne cikin wata wasika da shugaban majalisa, Bukola Saraki ya karanta a zauren majalisar a yau Laraba.

Kuma dai: Shugaba Buhari ya ki saka hannu kan wasu kudurori guda biyu

Kuma dai: Shugaba Buhari ya ki saka hannu kan wasu kudurori guda biyu
Source: Twitter

Buhari ya ce wasu daga cikin sassan kudirin kafa hukumar sufurin na kasa yana dauke da wasu ayyuka da a halin yanzu akwai hukumomin gwamnati na fanin sufuri da ke gudanar da wadannan ayyukan.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Ya ce, "Wasu ayyukan da aka lissafa cikin kudirin za su ci karo da ayyukan da hukumomi kamar NIMASA da NPA ke gudanarwa a halin yanzu saboda haka ya kamata a cire wadannan ayyukan.

"Ya kuma ce a rage kason kudin da hukumar za ta rika karba kamar yadda ya ke a sashi na 19(2)(d) daga kashi goma zuwa kashi biyar cikin dari domin haka ya ke cikin dokar cibiyar dalilai masu safarar kayayaki ta jirgin ruwa," inji shi.

A kan kudirin hukumar kula da tittunan tarayya na shekarar 2018, shugaban kasar ya ce ayyukan da ake son sabuwar hukumar ta rika yi suna karkashin Ma'aikatan Makamashi, Ayyuka da Gidaje ne a yanzu.

Ya ce kafa hukumar zai kwace ayyukan wasu sassan ma'aikatar.

"Ayyukan sabuwar hukumar za su ci karo da ayyukan da ma'aikan makamashi, ayyuka da gidaje keyi a yanzu."

Shugaban kasar ya ce kulawa da tittuna da nauyi ne da ya rataya a kan ma'aikatan Makamashi, Ayyuka da Gidaje saboda haka babu bukatar a kafa wata hukuma ta za ta sake maimaita wadannan ayyukan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel