Samari 3 sun yiwa Budurwa 'yar 18 fyade a jihar Legas

Samari 3 sun yiwa Budurwa 'yar 18 fyade a jihar Legas

Da yake dai Hausawa na cewa, Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, hakika hakan ta ke domin kuwa wasu samari uku sun tsunduma cikin tsaka mai wuya yayin da suka debo ruwan dafa kansu ta hanyar aikata babban laifin na fasadi a ban kasa.

Wata babbar kotun majistire da ke zamanta a yankin Ikeja na jihar Legas, ta bayar da umarnin garkame wasu samari uku a gidan kaso na Kirikiri biyo bayan mummunan laifin da suka aikata na yin rubdugu wajen fyade wata budurwa mai kimanin shekaru 18 a duniya.

Alkalin babbar kotun, Mai shari'a Olufunke Sule Amzat, shine ya bayar da umarnin wannan hukunci tare da gyara zamansa bisa kujerar naki ta bayar da belin ababen zargin kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Ababen zargin sun hadar da Wasiu Lawal mai shekaru 18, Tosin Taoreed mai shekaru 18 da kuma Peter Joseph mai shekaru 19 a duniya da dukkanin su sun kasance mazauna yankin Ikate na unguwar Ajah a jihar Legas.

Samari 3 sun yiwa Budurwa 'yar 18 fyade a jihar Legas

Samari 3 sun yiwa Budurwa 'yar 18 fyade a jihar Legas
Source: UGC

Jami'i mai shigar da kara a gaban kotu, Benson Emuerhi, ya bayar da shaidar cewa, ababen zargin sun aikata wannan mummunan ta'ada da misalin karfe 11.00 na daren ranar 18 ga watan Nuwamban da ya gabata a layin Eyiwuayi da ke mazaunar su ta Ikate.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Azal ta afkawa wannan Budurwa inda ta yi kacibus da miyagun uku a yayin da take kan hanyarta ta komawa gida bayan isar da aiken wani Kawun ta.

KARANTA KUMA: PDP na zargin wani sabon tuggu na tsige Saraki

A yayin da lamarin ke gaban Kuliya a halin yanzu, Mai shari'a Sule Amzat, ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Janairun sabuwar shekara mai gabatowa tare da bayar da umarnin garkame miyagun na tsawon makonni a gidan Dan Kande.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Larabar Tabawa ranar samu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar nan na shekarar badi a zauren majalisar dokoki ta tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel