Buhari ya kammala gabatar da kasafin kudin 2019, karanta lissafin

Buhari ya kammala gabatar da kasafin kudin 2019, karanta lissafin

Bayan awa daya a tsaye yana kwararo bayanai kan kasafin kudin shekarar 2019 na kudi Tiriliyan 8.83tr, yan majalisan PDP da na APC basu gushe suna iwu a cikin zauren majalisa ba.

Yayinda Saraki ke kokarin kamalla, yan majalisan suna ta ihun 'Sai Baba' wasu na wakokin nuna rashin yarda da Buhari suna wakokin zanga-zanga.

A Karshe a yanke shawara shugaba Buhari ya wuce tunda yan majalisan sun hana kakakin majalisar wakilai magana.

A yanzu haka ana wakar taken Najeriya domin baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar wucewa.

KU KARANTA: Adadin matasa maras aikinyi ya tashi daga miliyan 17.6 zuwa miliyan 20.9

Karanta jerin kudaden kasafin kudin filla-filla:

Shugaba Buhari ya gina kasafin kudin 2019 akan abubuwa gufa uku:

1. Farashin man fetur $60

2. Za'a fitar litan danyen mai lia milyan 2.3 a kowace rana

3. Farashin canjin dala N305/$1.

Jimillan kasafin kudin: N8.83trillion

Kudin biyan albashin ma'aikata – N4.04 trillion

Kudin biyan basussuka – N2.14 trillion

Kudaden ayyukan irinsu hanyoyi, inganta wutan lantarki, da sauransu - N2.031 Trillion

Biyan kudaden wadanda suka sanyawa gwamnati hannun jari irisu SUKUK – N120 billion

Kudin yan majalisa – N492.36 billion

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel