Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin tarayya, yan majalisa na kokarin cin mutuncin Buhari

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin tarayya, yan majalisa na kokarin cin mutuncin Buhari

An samu jinkiri a taron gabatar da kasafin kudin 2019 da shugaba Muhammadu Buhari zai yi da ranan Laraba, 19 ga watan Disamba, 2018 yayinda wasu yan majalisa suka fara shirin gudanar da zanga-zanga a zauren majalisa.

Yan majalisan musamman yan jam'iyyar adawa suna dauke da manyan takardu masu rubutu daban-daban suna shiga cikin zauren.

An shirya gabatar da kasafin kudin karfe 12 na rana.

Zuwa karfe 12:20 na rana, yan majalisan sun shiga ganawar sirri domin baiwa yan majalisan hakuri kada su ci mutuncin shugaban kasa.

KU KARANTA: Direban Keke Napep ya mayar da kudi miliyan daya da ya tsinta

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin tarayya, yan majalisa na kokarin cin mutuncin Buhari

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin tarayya, yan majalisa na kokarin cin mutuncin Buhari
Source: Depositphotos

Amma, da alamun an shawo kan al'amarin yayinda aka ga babban hadimin shugaba Buhari kan majalisar wakilai, Kawu Sumaila, yana fito da takardun da suka shiga da su.

Yayinda ake ganawar sirri, wani masoyin shugaba Buhari, Hanarabul Gudaji Kazaure, ya fito yana fadi da Hausa cewa "Ba zamu yarda wani yaci mutuncin Buhari ba." Ya tsinewa masu shirin haka.

Mun kawo muku rahoton Sabanin abinda ake sa ran gani da safiyar yau a majalisar dokokin tarayya, ma'aikatan majalisar dake zanga-zanga a makon nan sun bada wuri saboda shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel