Kasafin 2019: Osinbajo, ministoci da hadiman Buhari sun dira majalisa

Kasafin 2019: Osinbajo, ministoci da hadiman Buhari sun dira majalisa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ministoci da hadiman shugaba Buhari masu yawa sun isa zauren majalisa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Osinbajo da hadiman sun isa zauren majalisar ne da misalin karfe 11:50 na safe, yayin da ake sa ran shugaba Buhari zai iso zauren majalisar da misalin karfe 12:00 na rana.

Sai dai wasu rahotannin da suka iso wa legit.ng sun bayyana cewar sanatoci sun fara zaman majalisa bayan gajiya da jiran karasowar shugaba Buhari.

Kasafin 2019: Osinbajo, ministoci da hadiman Buhari sun dira majalisa

Osinbajo, ministoci da hadiman Buhari sun dira majalisa
Source: Depositphotos

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya jagoranci fara muhawara a majalisar bayan isowar sa da misalin 10:45 na safe.

Duk da Sanatocin sun fara tattauna wasu batutuwan, ana saka ran zasu katse zaman duk lokacin da shugaba Buhari ya karaso.

DUBA WANNAN: Kungiyar Boko Haram ta saki hotunan harin da ta kai a Maiduguri

An tsaurara tsaro a harabar majalisar da kewaye. Kazalika ba a ga motsin ma'aikatan majalisar dake gudanar da zanga-zanga ba tun cikin makon jiya.

Wata majiya ta ce isowar Buhari ta samu jinkir ne domin ganin an sasanta wata matsala da kan iya saka mambobin majalisar yi masa bore dan ya zo gabatar da kasafin kudin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel