Yanzu Yanzu: Tsoffin yan bindiga sun mamaye kofar majalisar dokoki, sun bukaci a biya su

Yanzu Yanzu: Tsoffin yan bindiga sun mamaye kofar majalisar dokoki, sun bukaci a biya su

- Tsoffin yan bindigan Niger Delta sun kai mamaya mashigin majalisar dokokin kasar inda suka bukaci a biyasu alawus dinsu

- Sun kuma nemi a dakatar da shugaban shirin bayar da tallafi ga tubabun yan bindiga, Birgediya Janar Paul Boroh (mai rtitaya)

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ke shirin tarban shugaban kasa Buhari wanda zai gabatar da kasafin kudin 2019

Wasu tsoffin yan bindigan Niger Delta sun kai mamaya mashigin majalisar dokokin kasar inda suka bukaci a biyasu alawus dinsu sannan suka nemai a dakatar da shugaban shirin bayar da tallafi ga tubabun yan bindiga, Birgediya Janar Paul Boroh (mai rtitaya).

Tsoffin yan bindigar sun kasance dake da kwalaye da rubutu irinsu, Ya Zama Dole Dokubo Ya Tafi sannan A Biya Mu Hakkinmu.

Yanzu Yanzu: Tsoffin yan bindiga sun mamaye kofar majalisar dokoki, sun bukaci a biya su

Yanzu Yanzu: Tsoffin yan bindiga sun mamaye kofar majalisar dokoki, sun bukaci a biya su
Source: Depositphotos

Masu zanga-zangan sun iso kofar majalisar dokokin ne yayinda majalisar ke shirin tarban shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai gabatar da kasafin kudin 2019.

Yayinda aka shirya gabatar da kasafin kudin da mislain karfe 11 na safe, masu zanga-zangan sun isa kofar majalisa tun karfe 7:30 na safe.

KU KARANTA KUMA: An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

Tsoffin yan bindigan sunce sun yi zanga-zangan ne domin janyo hankalin shugaban kasa akan ta’adin da ake yi a shirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel