Hukumar bunkasa Arewa maso Gabas: Dogara ya gabatarwa Buhari wata babbar bukata

Hukumar bunkasa Arewa maso Gabas: Dogara ya gabatarwa Buhari wata babbar bukata

- Hon. Yakubu Dogara ya bukaci shugaba Buhari da ya gaggauta kafa kwamitin gudanarwa na hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso Gabas

- Dogara ya ce bai kamata a rinka kawo banbance banbancen addini ko kabila a wajen zabar wakili ko shugaba ba

- Ya ce idan har hukumar bunkasa shiyyar Arewa mas Gabas ta fara aiki, hakan zai bunkasa rayuwar al'ummar shiyyar da kuma farfado da shiyyar

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kafa kwamitin gudanarwa na hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC), don ganin cewa an bunkasa yankin da jama'ar da ke cikinsa.

Dogara, wanda ya bayyana hakan a wani shirin gabaytar da ayyukan shiyya, da Binta Bello, mataimakiyar shugabar marasa rinjaye a majalisar, da ta kaddamar a garin Kaltungo, jihar Gombe, a ranar Talata, ya kuma bukaci masu kada kuri'a da su zabi 'yan takara da zasu bunkasa yankunansu da rayuwakansu.

Ya kara da cewa bai kamata a rinka kawo banbance banbancen addini ko kabila a wajen zabar wakili ba, ma damar mutum zai iya aiwatar da aikinsa cikin hazaka, to kuwa shine ya kamata jama'a su zaba don kawo masu ci gaba.

KARANTA WWANNAN: Gaskiyar magana: Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin makiyaya da manoma - Miyetti Allah

Saraki, Buhari da Dogara

Saraki, Buhari da Dogara
Source: UGC

Dogara ya jaddada cewa, bayan da ya fahimci sirrin da ke tattare da yiwa al'ummar mazabarsa aiki cikin gaskiya, da kuma shayar da su romon demokaradiyya ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba, wannan ne dalili da ya sanya jama'ar tasa suka zabe shi har sau uku don ya wakilce su, a dalilin hakan, ya samu damar zama kakakin majalisar wakilan tarayyar.

Ya bayyana cewa a dalilin zamansa kakakin majalisar, ba wai jihar Bauchi kadai ta amfana ba, shiyyar Arewa maso Gabas ta samu tagomashi, sakamakon yadda ya samar da hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC).

Kakakin majalisar wakilan tarayyar ya bukaci al'ummar shiyyar Gombe ta Kudu a majalisar dattijai cewa da zasu sake zabar Binta Bello, wacce a cewarsa tana da son jama'a da ci gabansu, a wannan dalilin ma ya sa har ta zama mataimakiyar shugaban marasa rinjaye.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel