Kai tsaye: Yan zanga-zanga a majalisa sun cika alkawarinsu, sun bada wuri Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019

Kai tsaye: Yan zanga-zanga a majalisa sun cika alkawarinsu, sun bada wuri Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019

Sabanin abinda ake sa ran gani da safiyar yau a majalisar dokokin tarayya, ma'aikatan majalisar dake zanga-zanga a makon nan sun bada wuri saboda shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019.

Ana sauraron zuwan shugaba Buhari a karfe 11 na safe inda yan majalisar dattawa da na wakilai zasu taru a zauren majalisar wakilai.

Jami'an hukumar yan sanda, DSS, masu tsaron fadar shugaban kasa, jami'an hukumar FRSC, na hukumar NSCDC sun mamaye majalisar.

Magatakardan majalisar dokokin tarayya, Mr Mohammed Sani-Omolori, na cikin majalisar tare da babban hadimin shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Ita Enang, kan yadda zasu shigo da shugaba Buhari.

KU KARANTA: Yayinda Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudi, ana kokarin tsige Saraki - PDP

Kamar yadda sukayi alkawari jiya, ma'aikatan majalisar karkashin kungiyar ma'aikatar majlisun Najeriya, basu fito zanga-zanga ba yau kamar yadda sukayi a kwanakin makon nan.

A ranan Talata, ma'aikatan sun yanke wuta, magudanar ruwa kuma sun rufe hanyar shiga majalisan inda suka ce babu wanda za'a amince ya shiga majalisar har sai an basu hakkinsu.

Daga baya sai aka smau labari wasu yan majalisu sun samu hanyar shiga cikin zauren majalisa ta baya kuma suka zanna kan zuwan Buhari majalisar yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel