Yayinda Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudi, ana kokarin tsige Saraki - PDP

Yayinda Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudi, ana kokarin tsige Saraki - PDP

Rikicin siyasa ya sake kunno kai a majalisar dokokin tarayya yayinda jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa akwai wani sabon tuggu da ake shiryawa ta hanyar amfani da jami'an yan sanda da DSS wajen tsoge shugbana majalisar dattawa Bukola Saraki.

Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, ya bayyana cewa irin abun da DSS tayi a kwanakin baya har aka cire shugabanta, Lawal Daura, ake son maimaitawa domin daburta lissafin yakin neman zaben shugabancin kasan da jam'iyyar ke yi.

Game da cewarsa: "Daga cikin kaidin da suke shiryawa shine amfani da yan sanda da DSS wajen kalawa Saraki sharri domin daburta lissafin yakin neman zaben shugaban kasa jam'iyyar PDP. wannan ba zai yiwu ba saboda yan Najeriya suna bayan PDP."

KU KARANTA: Kai tsaye: Yan zanga-zanga a majalisa sun cika alkawarinsu, sun bada wuri Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019

Jam'iyyar adawar ta bayyana cewa ta samu labarin cewa fadar shugaban kasa da shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), suna kokarin kaiwa Bukola Saraki hari.

Sanatocin da sukayi magana da jaridar THISDAY a daren jiya kan wannan zargi sunyi gargadin cewa wannan abu da ake shirya ka iya zama cikas ga kasafin kudin 2019 da Buhari zai gabatar a rana Laraba.

Yace: "Ban tunanin akwai hikima cikin hakan, dubi ga yadda hakan zai shafi kasafin kudin 2019 da za'a gabatar a ayu."

Wani Sanata da aka sakaye sunansa yace: Ko shakka babu ba zamu yarda da hakan ba, kuma hakan ba zai kyautatu da mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel