An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

- An tsaurara matakan tsaro a kewayen majalisar dokokin kasar gabannin ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Buhari zai gabatar da kasafin kudin a gaban majalisun dokokin kasar a yau

- An zuba tawagar hukumomin tsaro a mashigin majalisar guda uku

An tsaurara matakan tsaro a kewayen majalisar dokokin kasar gabannin ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari don gabatar da kasafin kudin 2019.

Ana sanya ran Buhari zai gabatar da kasafin kudin a gaban majalisun dokokin kasar biyu a ranar Laraba, 19 ga watan Disamba da karfe 11:00 na safe.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa an zuba tawagar hukumomin tsaro a mashigin majalisar guda uku.

An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019
Source: Depositphotos

Inda aka zuba matakan tsaron sune babban kofar majalisar dake kallon sakatariyar tarayya, mashigin ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya a Aso Drive da kuma kofar baya dake hada majalisar da fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas

Wadanda aka bayar da suneyensu ne kadai ake bari su shiga bayan jami’an tsaro tantance su da kyau.

An kuma takaita jigilar ababen hawa zuwa nay an majalisa da manyan mataikatan majalisar dokokin.

Gabatar da kasafin kudin na zuwa ne a kwana na uku cikin hudun da ma’aikatan majalisar suka diba don yin yajin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel