Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas

Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas

- Hadimin Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra, Mista Chidi Obidiegwu ya kaddamar da yunkurin yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen domin yin tazarce a 2019

- Obidiegwu ya bayyana hakan a ranar Talata, a wani taron kungiyar manema labarai a Awka, jihar Anambra

- Obidiegwe yace kamfen din da yake yiwa Buhari domin ci gaban yan Igbo ne

Wani babban hadimin Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra, Mista Chidi Obidiegwu ya kaddamar da yunkuri na yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen domin yin tazarce a 2019.

Obidiegwu ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Disamba a wani taron kungiyar manema labarai a Awka, jihar Anambra.

Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas

Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas
Source: UGC

Tare da rakiyan George Okoye, tshon dan takarar kujran shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, Obidiegwe yace kamfen din da yake yiwa Buhari domin ci gaban yan Igbo ne.

Obidiegwu wanda ya tuna da irin gawagwarmayar da yan Igbo suka shat un bayan gama yakin basasa na Najeriya, yace yan Igbo basu shirya wasan adawa a Najeriya da wasa ba kuma.

KU KARANTA KUMA: Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas

Ya yaba ma ci gaban da Buhari ya kawo a yankin kudu maso gabas, cewa shugaban kasar ya nufi mutanen yankin da alkhairi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel