Gwamnati na cigaba da tattaunawa da ASUU kuma an kusa cin ma maslaha – Ngige

Gwamnati na cigaba da tattaunawa da ASUU kuma an kusa cin ma maslaha – Ngige

Mun ji labari Ministan kwadago na Kasa, Dr Chris Ngige, ya bayyana cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ta na cigaba da zama da Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’o’i domin kawo karshen yajin aikin da aka yi.

Gwamnatin na cigaba da tattaunawa da ASUU kuma an kusa cin ma maslaha – Ngige

Ngige yace kwanan nan Gwamnati za ta cin ma matsaya da ASUU
Source: Twitter

Chris Ngige yayi wannan jawabi ne a jiya Ranar Talata inda ya tabbatar da cewa ana cigaba da samun masalaha wajen tattaunawar da Gwamnati ke yi da Malaman makaranta. Ngige ya karyata rahotan cewa sun gaza cin ma matsaya

Dr. Ngige yace tattaunawar da su ke yi da Kungiyar ASUU yana tafiya yadda ya kamata, akasin abin da aka rika yadawa a gidan jaridu na cewa Malaman Jami’o’in sun tashi baram-baram a taron da aka yi a cikin farkon wannan makon.

Darektan yada labarai na ma’aikatar kwadago na kasar, Samuel Olowookere, shi ya fitar da wannan jawabi inda ya tabbatar da cewa Ministan kasar ya zauna da Kungiyar ASUU na sa’a biyu inda su ka tattauna cikin fahimtar juna.

KU KARANTA: An tashi baram-baram a taron ASUU da gwamnati a Abuja

Ministan yace ba baram-baram aka tashi a zaman da aka yi a Ranar Litinin ba, Jami’in Ma’aikatar yace an tashi daga zaman ne bayan Hukumomin Gwamnati da aka mikawa takardun yarjejeniyar yajin aikin na ASUU sun karasa aikin su.

Ngige ta bakin Olowookere ya kara da cewa, Kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya sun amince da matsayar da aka cin ma a taron, don haka ne a aka bada lokaci domin sake duba yarjeniyar kafin bikin Kirismeti inji Ministan na kwadago.

A jawabin dai, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ana samun nasara wajen zaman sulhun d ake yi tsakanin su da Malaman makaratun Jami’o’i na kasar. Gwamnati tana sa rai a shawo kan matsalar a koma a cigaba da karatu a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel