Babu masu lura da Hukumomin NDIC da FIRS a Najeriya tun 2015

Babu masu lura da Hukumomin NDIC da FIRS a Najeriya tun 2015

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa yanzu shekaru 3 kenan da nema ba tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu manyan mukamai a Hukumomin Gwamnatin Tarayya ba.

Babu masu lura da Hukumomin NDIC da FIRS a Najeriya tun 2015

Shugaban Hukumar FIRS na Najeriya Babatunde Fowler
Source: Depositphotos

A tsawon shekarun da wannan Gwamnati tayi, babu masu lura da abin da shugabannin Hukumomin NDIC da kuma FIRS su ke yi. Tun a tsakiyar 2015 ne aka ruguje Majalisar da ke sa ido a wadannan Hukumomi ba tare da an nada wasu ba.

Kamar yadda Jaridar ta rahoto, Ma’aikatan Hukumar FIRS mai tarawa Najeriya kudin shiga, sun nuna cewa ba su bukatar a nada Majalisar da ke lura da Hukumar domin kuwa hakan zai hana su aikin da su ka sa gaba na tatso kudi a fadin Kasar.

Shugaban Hukumar FIRS na kasa, Babatunde Fowler, yana cigaba da kokarin ganin yadda za a toshe kafofin karbar haraji a Najeriya. Yanzu haka Hukumar ta na sa ran tatso Naira Tiriliyan 5.3 a bana wanda ba a taba yi ba tarihin kasar nan.

KU KARANTA: Atiku yace cin hanci ya samu gindin zama a gwamnatin Buhari

Haka kuma a Hukumar NDIC mai lura da kudin da ke shiga hannun bankuna ba su da masu sa masu idanu tun da wannan Gwamnatin Buhari ta kafu. Wannan ta sa dole shugabannin Hukumar su ke hulda kai tsaye da Ministar kudi ta Najeriya.

Yanzu dai ana jira Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Majalisar da za ta rika lura da NDIC din bayan da Sanatoci su ka tantance sunayen wadanda aka aika mata. Ra’ayin masana dai ya banbanta game da tasirin wannan mataki.

Irin su Hukumar FIRS dai sun dauki Ma’aikata fiye da 800 a cikin shekaru 3 ba tare da kafuwar Majalisar da ke sa idanu a Hukumar ba. Wannan dai ya sabawa tsarin mulkin Najeria da kuma dokar aiki na FIRS.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel