Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas

Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas

- Yakubu Dogara yayi kira ga mutanen arewa maso gabas da su zabi Atiku Abubakar

- Kakakin majalisar wakilan yayi ikirarin cewa gwamnatin Buhari ta kawo rashin tsaro

- Dogara yace ya zama dole mutane su yanke shawarar ko suna son ci gaba da irin wannan tsari na rayuwar da suke ciki

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yayi ikirarin cewa lamarin rashin tsaro ya karu sosai a lokacin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sannan yayi kira ga mutanen arewa maso gabas da su zabi Atiku Abubakar.

Vanguard ta ruwaito cewa Dogara ya fadi hakan ne a Gombe yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party ta gudanar da gangaminta na yankin.

Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas

Zabar Buhari zai haifar da rashin tsaro – Dogara ga mutanen arewa maso gabas
Source: UGC

Ya nace cewa lallai zaben 2019 game da rashin tsaro ne inda yayi ikirarin cewa abubuwa sun dada tabarbarewa.

Dogara yace lallai kasar ta shiga wani irin yanayi a karkashin gwamnatin Buhari domin a cewarsa a yanzu kimanin yara miliyan 13 ne basa zuwa makaranta kuma cewa cikinsu yara 1.3 daga jiharsa ta Bauchi suke.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya - Atiku

Kakakin majalisar yace abubuwa sun fi daidaita a lokacin gwamnatin PDP inda ya zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kasa kare rayukan mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel